Allah Ya yi wa Maryam Bayero mahaifiyar Sarkin Kano rasuwa
Allah Ya yi wa Hajiya Maryam Ado Bayero matar tsohon sarkin Kano marigayi Ado Bayero.
Mai Babban Daki mahaifiya ce ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Majiyoyin masarautar Kano da suka tabbatar wa BBC da labarin rasuwarta, sun ce ta rasu ne a ranar Asabar a ƙasar Masar.
Majiyoyin sun ce ta rasu ne misalin ƙarfe tara na safiyar Asabar. Kuma zuwa gobe ake sa ran yin jana'izarta bayan iso da gawarta zuwa Najeriya daga Masar
Babu wata sanarwa kawo yanzu da ta fito daga Masarautar Kano ko gwamnatin Kano game da labarin rasuwar Hajiya Maryam Ado Bayero.
Comments
Post a Comment