An kama mutumin da ya shafa wa mutum 22 cutar korona
An kama wani mutum a Spain da ake zargi da cin zarafi bayan ya yaɗa wa mutum 22 cutar korona.
Mutumin mai shekara 40 an yi zargin cewa ya ci gaba da zuwa wurin aikinsa da kuma motsa jiki duk da yana tari kuma zafin jikinsa ya kai sama da 40C.
An bayyana cewa yana yawonsa a wurin da yake aiki a Majorca, yana cire takunkumi idan zai yi tari tare da faɗa wa abokan aikinsa cewa zai shafa masu korona.
Abokan aikin biyar da wasu mutum uku a wurin da yake zuwa motsa jiki sun kamu da cutar.
Wasu mutum 14 cikin ƴan uwansa sun kamu da cutar ciki har da ɗan shekara ɗaya.
Ƴan sandan Spain cikin wata sanarwa sun ce mutumin ya daɗe da nuna alamun cutar, amma ya ƙi killace kansa a gidansa da ke Manacor.
An yi masa gwaji, amma ya ci gaba da wurin aiki da motsa jiki yayin da yake jiran sakamako ya fito.
Ƴan sandan sun ce ya bijerewa abokan aikinsa da ke faɗa masa ya tafi gida. Yana cire takunkumin fuska sai ya yi tari ya fada masu cewa “zan shafa maku cutar korona.”
Comments
Post a Comment