Posts

Showing posts from May, 2021

Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Nigeria

Image
Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya. Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita a yau Alhamis. Naɗin na zuwa ne kwana shida bayan rasuwar Janar Ibrahim Attahiru mai jagorantar rundunar. Janar Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna, da kuma wasu mutum 11 cikin har da janar-janar uku. W ane ne Manjo Janar Farouk  Yahaya? An haifi Manjo Janar Farouk Yahaya a garin Sifawa na karamar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya a shekarar 1966. Ya shiga aikin soja a 1985 a matsayin dan aji na 37 inda ya kammala karatun soji a ranar 22 ga watan Satumba na 1990. Ya samu karin girma a rundunar soji kamar haka: Laftana - ranar 27 ga Satumba 1990 Kyaftin - ranar 27 ga watan Satumba 1994 Manjo - ranar 27 ga watan Satumba 1998. Laftanar Kanar - ranar 27 ga watan Satumba 2003. Kanar - ranar 27 ga watan Satumba 2008 Birgediya Janar - ranar 27 ga watan...

MAJALISAR DATTAWA TA UMARCI JAMB ta dakatar da amfani da NIN wajen rajista

Image
: NIMC Majalisar Dattawan Najeriya ta umarci Ma'aikatar Ilimi da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta Joint Admission and Matriculation Board (JAMB) da su sake duba shirinsu na amfani da lambar ɗan ƙasa ta National Identity Number (NIN). 'Yan majalisar sun ba su umarnin ne a yau Talata domin ƙara wa'adin rajistar jarrabawar ko kuma soke shirin haɗa rajistar da kuma NIN ga ɗalibai har sai an samar da wani tsari cikakke na samun lambar ta ɗan ƙasa. Kazalika, ƙudirin ya ƙunshi umarni ga Ma'aikatar Ilimi da hukumar samar da NIN ta National Identity Management Commission (NIMC) da su samar da wani tsari mai sauƙi da zai bai wa ɗaliban samun lambar ta NIN a makarantunsu. A 'yan kwanakin nan ne JAMB ta mayar da NIN wajibi ga duk ɗalibin da ke son shiga jami'a a ƙasar. Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra wanda ya gabatar da ƙudirin, ya ce matakin na JAMB "rashin tausayi ne kuma ya yi wuri". Ƙudirin ya bayyana cewa shirin na JAMB y...