MAJALISAR DATTAWA TA UMARCI JAMB ta dakatar da amfani da NIN wajen rajista
: NIMC
Majalisar Dattawan Najeriya ta umarci Ma'aikatar Ilimi da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta Joint Admission and Matriculation Board (JAMB) da su sake duba shirinsu na amfani da lambar ɗan ƙasa ta National Identity Number (NIN).
'Yan majalisar sun ba su umarnin ne a yau Talata domin ƙara wa'adin rajistar jarrabawar ko kuma soke shirin haɗa rajistar da kuma NIN ga ɗalibai har sai an samar da wani tsari cikakke na samun lambar ta ɗan ƙasa.
Kazalika, ƙudirin ya ƙunshi umarni ga Ma'aikatar Ilimi da hukumar samar da NIN ta National Identity Management Commission (NIMC) da su samar da wani tsari mai sauƙi da zai bai wa ɗaliban samun lambar ta NIN a makarantunsu.
A 'yan kwanakin nan ne JAMB ta mayar da NIN wajibi ga duk ɗalibin da ke son shiga jami'a a ƙasar.
Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra wanda ya gabatar da ƙudirin, ya ce matakin na JAMB "rashin tausayi ne kuma ya yi wuri".
Ƙudirin ya bayyana cewa shirin na JAMB ya saka ɗaliban Najeriya masu son shiga jami'o'i cikin tasku.
Wasu iyayen ɗaliban sun faɗa wa BBC yadda shirin ke wahalar da su da yaran nasu sakamakon rashin sauƙi wajen shigar da lambar NIN ɗin yayin rajistar jarrabawar
Comments
Post a Comment