Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Nigeria

Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya. Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita a yau Alhamis. Naɗin na zuwa ne kwana shida bayan rasuwar Janar Ibrahim Attahiru mai jagorantar rundunar. Janar Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna, da kuma wasu mutum 11 cikin har da janar-janar uku. W ane ne Manjo Janar Farouk Yahaya? An haifi Manjo Janar Farouk Yahaya a garin Sifawa na karamar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya a shekarar 1966. Ya shiga aikin soja a 1985 a matsayin dan aji na 37 inda ya kammala karatun soji a ranar 22 ga watan Satumba na 1990. Ya samu karin girma a rundunar soji kamar haka: Laftana - ranar 27 ga Satumba 1990 Kyaftin - ranar 27 ga watan Satumba 1994 Manjo - ranar 27 ga watan Satumba 1998. Laftanar Kanar - ranar 27 ga watan Satumba 2003. Kanar - ranar 27 ga watan Satumba 2008 Birgediya Janar - ranar 27 ga watan...