Posts

Showing posts from April, 2021

YADDA MATASA SUKA KONA OFISHIN YAN SANDA A JAHAR SOKOTO

Image
Rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar mutum daya tare da konewar wani ofishin yan sanda da wasu motoci biyu a karamar hukumar Kware. Mai magana da yawun rundunar yan sandan ASP Abubakar Sani cikin wata sanarwa ya ce lamarin ya faru ne bayan da wasu gungun mutane suka je chaji ofis din inda suka nemi a saki wasu mutum biyu da ake zargi masu garkuwa ne. Sanusi ya ce tun farko an kama wadanda ake zargin inda ake gudanar da bincike a kansu saboda samunsu da hannu a garkuwa da mutane a yankin. Ya bayyana cewa gungun akasarinsu matasa sun je ofishin yan sandan inda suka rika ihu tare da neman a saki mutanen biyu da ke tsare. Kakakin rundunar ya kara da cewa mataan sun ci karfin jami'an tsaron da ke kula da ofishin inda suka cinna masa wuta har da motar DPO da wasu motocin yan sanda biyu. A cewarsa, matasan sun halaka daya daga cikin mutanen da ake zargi masu garkuwa ne tare da raunata dayan. Kawo yanzu, ba a kama ko mutum daya ba amma ana ci gaba da gudanar...

Za a biya matasa kimanin naira dubu arba'in idan suka amince a yi musu rigakafin korona

Image
Za a biya matasa kimanin naira dubu arba'in idan suka amince a yi musu rigakafin korona                  Copyright: Getty Images Wata jiha a Amurka ta ce za ta bai wa matasa tukwicin dalar Amurka 100 kwatankwacin kimanin naira dubu arba'in idan suka amince aka yi musu allurar rigakafin korona. Jihar West Virginia ta ce tana fatan ba da tukwicin ga yan shekara 16 zuwa 35 domin basu kwarin gwiwar zuwa a yi musu allurar. A cewar gwamnan jihar, Jim Justice, matasa suna da rawar takawa a yaƙi da annobar ta korona. Jihar tana daga cikin jihohin Amurka da aka tsara yi wa jama'a da yawa allurar rigakafin sai dai lamarin ya fuskanci tsaiko a baya-bayan nan. Akwai fargabar cewa matasa na iya nuna rashin damuwa da zuwa yin rigakafin. Ba da kudin na nufin mutanen da aka yi wa allurar da ke cikin rukunin za su iya samun dalar Amurka 100 da riba a wani lokaci nan gaba. Za kuma a bai wa duk wanda shekarunsa suka kai 16 zuwa 35 da tuni aka yi mus...

An kama mutumin da ya shafa wa mutum 22 cutar korona

Image
An kama wani mutum a Spain da ake zargi da cin zarafi bayan ya yaɗa wa mutum 22 cutar korona. Mutumin mai shekara 40 an yi zargin cewa ya ci gaba da zuwa wurin aikinsa da kuma motsa jiki duk da yana tari kuma zafin jikinsa ya kai sama da 40C. An bayyana cewa yana yawonsa a wurin da yake aiki a Majorca, yana cire takunkumi idan zai yi tari tare da faɗa wa abokan aikinsa cewa zai shafa masu korona. Abokan aikin biyar da wasu mutum uku a wurin da yake zuwa motsa jiki sun kamu da cutar. Wasu mutum 14 cikin ƴan uwansa sun kamu da cutar ciki har da ɗan shekara ɗaya. Ƴan sandan Spain cikin wata sanarwa sun ce mutumin ya daɗe da nuna alamun cutar, amma ya ƙi killace kansa a gidansa da ke Manacor. An yi masa gwaji, amma ya ci gaba da wurin aiki da motsa jiki yayin da yake jiran sakamako ya fito. Ƴan sandan sun ce ya bijerewa abokan aikinsa da ke faɗa masa ya tafi gida. Yana cire takunkumin fuska sai ya yi tari ya fada masu cewa “zan shafa maku cutar korona.”

YADDA AKE DAUKAR SABON FILM DIN ACTOR PRABHAS MAI SUNA SALLER ZA'AFIDDASHI (APRIL 2022)

Image

Allah Ya yi wa Maryam Bayero mahaifiyar Sarkin Kano rasuwa

Image
Allah Ya yi wa Hajiya Maryam Ado Bayero matar tsohon sarkin Kano marigayi Ado Bayero. Mai Babban Daki mahaifiya ce ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero. Majiyoyin masarautar Kano da suka tabbatar wa BBC da labarin rasuwarta, sun ce ta rasu ne a ranar Asabar a ƙasar Masar. Majiyoyin sun ce ta rasu ne misalin ƙarfe tara na safiyar Asabar. Kuma zuwa gobe ake sa ran yin jana'izarta bayan iso da gawarta zuwa Najeriya daga Masar Babu wata sanarwa kawo yanzu da ta fito daga Masarautar Kano ko gwamnatin Kano game da labarin rasuwar Hajiya Maryam Ado Bayero.

Falalar kwanaki 10 Wata ne da ake son Musulmi ya siffantu da bautar Allah da addu'o'i tare da neman gafara ga Mahalicci.

Image
Watan Ramadan baki ɗayansa na ƙunshe da falala tun daga 10 na farko na watan zuwa 10 na tsakiya da kuma kwanaki mafi daraja a 10 ta ƙarshe. Shiekh Abubakar Baban Gwale ya yi wa BBC bayani kan falalar 10 ta tsakiya da kuma abubuwan da ake son Musulmi ya himmatu. Malamin ya ce watan Azumi wata ne da ake ƙara alherin mumuni a cikinsa - duk lokacin da aka ƙara kwanaki alherinsa yana kara ƙaruwa. "Manzon Allah (SAW) ya ce farkon watan Ramadan rahama ne, tsakiyarsa kuma gafara ce ƙarshensa kuma 'yanta mutum ne daga wuta." Malamin ya ce idan aka shiga zango na gafara ba wai ana goge rahama ba ne - ana son mutum ya nunka ibada domin ya hada rahama da kuma gafara tare da kara kusanci ga Allah. Ci gaban kwanakin Ramadan ƙarin samun falala ne da kuma kusantar dare mai albarka na Laylatul kadri. Ayyukan Ibadah da ake son mutum ya dage Shiekh Abubakar Baban Gwale ya bayyana ayyukan Ibadah da ake son mutum ya dage akansu kamar haka: Musulmi ya dage da sallolin farilla da Al...

An yi wa wasu mata-maza 'yan Kano tiyatar sauya jinsi a Sokoto

Image
Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce za ta gina cibiyar kula da masu fama da larurar mata-maza a jihar. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yayin da yake karɓar ƴan asalin jihar maza da mata su shida da aka yi wa aiki a asibitin koyarwa na Jami'ar Sokoto a gidan gwamnati a ranar Laraba. A lokuta da dama masu fama da wannan lalura kan gaza nema wa kansu lafiya ne saboda ɗawainiyar kuɗaɗen da ake kashewa kafin samun lafiya. Gwamna Ganduje ya ce saboda ƙarancin likitoci da ke da ƙwarewa a wannan fannin a Kano, gwamnatinsa za ta haɗa gwiwa da cibiyar kula da masu lalurar mafitsara da ƙoda ta Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto, don horarwa wajen kula da masu fama da wannan larura. "Wannan ya zama dole ne a wuyan gwamnati domin a taimaka, saboda wannan al'amari ne da bayan ya shafi lafiyarsu ya kuma shafi hanyar rayuwarsu da tunaninsu. Za mu sa ɗamba domin gina wannan cibiya ta yi wa mata-maza aiki domin a warkar da su. "Za mu ƙulla ƙawance t...

GWANNAN ZAMFARA YAYI GANAWAR SIRRI DA HAFSON SOJIN NIGERIA

Image
zamfara governor 

HUTONAN UMMI RAHAB KYAWAWA

Image
Masha Allah ummi rehab tasaki wasu kyawawan photos Nata a shafinta na instagram